'Yan wasan Turkiyya mata sun doke na Finlan da ci 3 da 0

'Yan wasan Turkiyya mata sun doke na Finlan da ci 3 da 0

A wasan rukuni na 4 na Gasar Kwallon Raga ta Mata ta Turai ta 2021, 'yan wasan Turkiyya sun doke na Finlan da ci 3 da 0.

A wasan da aka buga a filin wasanni na BT Arena da ke Romaniya, 'yan wasan Turkiyya sun fara motsawa da kwarin gwiwa inda a zagayen farko suka yi nasara da ci 25 da 19.

A zagaye na 2 kuma sun yi nasara da ci 25 da 12, a zagaye na 3 kuma da ci 25 da 15 suka wuce abokan karawarsu.

'Yan wasan na Turkiyya mata sun doke na Sabiya, Romaniya, Kuroshiya da Bulgari. Za kuma su fafata da Holan a wasan su na gaba.

 

News Source:   ()