'Yan wasan Turkiyya sun sami kambi 19 a gasar tsalle-tsalle ta kasa da kasa

'Yan wasan Turkiyya sun sami kambi 19 a gasar tsalle-tsalle ta kasa da kasa

Bayan kammala gasar wasannin tsalle-tsalle ta Balkan karo na 74 a garin Smederevo na kasar Sabiya, 'yan wasan Turkiyya sun tashi da kambin zinariya 4, na azurfa 9 da tagulla 6.

Bayan fafatawar kwanaki 2 an kammala gasar wasannin tsalle-tsalle ta kasashen Balkan.

Turkiyya da ta fafata a wasanni sama da 400 tsakanin kasashen duniya 19 ta zami kasa ta 2 mafi yawan kambi bayan Girka. Haka zalika ita ce ta zo ta 5 wajen yawan maki  a gasar.

News Source:   ()