Babu wanda aka samu da Covid-19 a Galatasaray

Babu wanda aka samu da Covid-19 a Galatasaray

An sanar da cewa gwajin kwayar cutar corona da aka yi wa wasu 'yan wasan kungiyar kwallon kafar Galatasaray ya nuna babu wanda keda cutar.

Kamar yadda kungiyar mai alamar alunin rawaya da ja ta yada a shafinta na yanar gizo ta gudanar da gwaje-gwajen kwayar cutar Covid-19 akan 'yan wasanta, masu horarwa da kuma masu bayar da shawara ga kungiyar.

A gwaje-gwajen ba'a samu kowa dauke da cutar ba.

 

News Source:  www.trt.net.tr