Baturke ya lashe gasar ninkaya ta kasa da kasa

Baturke ya lashe gasar ninkaya ta kasa da kasa

Dan kasar Turkiyya Emre Sakci ya lashe gasar kasa da kasa ta zakarun ninkaya a nisan mita 50.

A fafatawar da aka yi a Budapest Babban Birnin Hungary, Baturke Emre Sakci mai shekaru 22 ya samu nasarar lashe kambin zinare.

Emre Sakci da zai wakilci Turkiyya a wasannin tsalle-tsalle na Olympics da za a gudanar a shekara mai zuwa a Tokyo Babban Birnin Japan, ya doke dan kasar Birtaniya Adam Peaty wanda ya zo na 2 a gasar.

 

 

News Source:   ()