Corona: Ana muhawara game da makomar kungiyoyin kwallon kafa na Italiya

A kasar Italiya d ta kasance daya daga cikin kasashen da annobar Corona ta yadu sosai ana tattaunawa kan makomar kungiyoyin kwallon kafa na kasar.

Ana sa ran babban taron da Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Italiya za ta gudanar zai samar da taswira game da makomar kungiyoyin.

Amma kafin a gudanar da taron wasu bayanai masu jan hankali sun fito daga kafafan yada labaran Italiya.

Ana bayyana cewar kungiyoyin Torino, Sampdoria,Genoa, Bologna, Parma, SPAL, Brescia, Udinese da Fiorentina za su janye daga gasar Seria A.

An kuma fadi cewar wannan mataki da kungiyoyin 8 za su dauka zai haifar da illolin da ba za taba hasashensu ba.

A gefe guda kuma kungiyar Fiorentina ta fitar da sanarwa ta shafinta na yanar gizo inda ta karyata labaran da aka fitar na za ta janye daga Sirie A.

 

News Source:  www.trt.net.tr