Corona: Darajar kungiyoyin kwallon kafa na Turai za ta karye

Corona: Darajar kungiyoyin kwallon kafa na Turai za ta karye

Sakamakon annobar Corona (Covid-19), ana hasashen darajar kungiyoyin kwallon kafa na Turai za ta karye da kaso 20 zuwa 25.

Binciken da Cibiyar KPMG Football ta gudanar ya duba darajar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai 32 tare da binciken yadda Corona ta shafe su.

Binciken ya nuna cewar kungiyoyin Faransa ne za su fi kowadanne lalacewa a nahiyar Turai inda Olympique Lyon za ta karye da kaso 27,5 sai kungiyar PSG da kaso 25,4.

A jerin sunayen kungiyoyin akwai kungiyar Galatasaray ta Turkiyya wadda darajarta za ta karye da kaso 23,3 da kuma Besiktas da za ta karye da kaso 20,2.

News Source:  www.trt.net.tr