Corona ta kama Telles da ke taka leda Manchester United

Corona ta kama Telles da ke taka leda Manchester United

Cutar Corona (Covid-19) ta kama dan wasa da ke saka rigar kungiyar Mancheter United.

Mai horar da 'yan wasan Manchester United Ole Gunnar Solskaer ya shaida cewar Tells da bai samu damar buga wasan da aka buga da Leipzig a gasar Zakarun Turai ba, ya kamu da cutar Corona.

Solskjaer ya ce dan wasan bai nuna alamun yana dauke da cutar ba, kuma yana cikin yanayi mai kyau.

Dan wasan dan kasar Barazil mai shekaru 27, ya taba saka rigunan kungiyar Galatasaray da ke Turkiyya da kuma Porto da kasar Portugal inda daga nan ya koma Manchester United.

News Source:   ()