Dan tseren babur dan kasar Turkiyya Toprak Razgatlıoğlu ya yi hatsari

Dan tseren babur dan kasar Turkiyya Toprak Razgatlıoğlu ya yi hatsari

Dan tseren babur dan kasar Turkiyya Toprak Razgatlıoğlu ya yi hatsari yayin da ya ke rangadin motsa jiki a Spain domin gasar Superbike ta Duniya.

Kamar yadda Tarayyar Gasar Tseren Babura ta Kasar Turkiyya ta sanar Toprak, ya yi hatsari da Babur a yayinda yake tukin motsa jiki a kelenkeluwa ta 13 a da'irar Catalunya-Barcelona a safiyar yau.

Toprak wanda ya fadi daga Babur an duba shi nan take daga bisani kuma anka garzaya dashi asibiti.

An sanar da cewa bai samu halartar tseren babur din da aka yi jiya ba.

 

News Source:   ()