Gomis ya suma ana tsaka da buga wasan kwallo

Gomis ya suma ana tsaka da buga wasan kwallo

Dan wasan kwallon kafa dan kasar Faransa da ke sanyawa kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya riga Bafetimbi Gomis, ya suma ana tsaka da wasan da suke bugawa da kungiyar Al Ahli Jeddah.

Dan wasan ya yanke jiki ya fadi a minti na 12 da fara wasan.

Jami'an lafiya sun kai wa Gomis dauki nan da nan bayan ya fadi, kuma ya ci gaba da buga wasa har minti na 90.

Bayan an daga dan wasan, ya murmure tare da ci gaba da wasansa.

A lokacin da Gomis yake sakawa Galatasaray riga ma ya taba suma a wasan da suka buga da Kasimpasa.

News Source:   ()