Juventus ta yi wa Sassuolo wankin babban bargo

Juventus ta yi wa Sassuolo wankin babban bargo

A mako na 17 na gasar Zakarun Italiya ta Serie A, kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta doke takwararta ta Sassuolo da ci 3 da 1.

A wasan da aka fafata a filin wasa na Allianz da ke Torino, Juventus ta barje gumi da kungiya mai kuri ta Sassuolo.

A zagaye na biyu na wasan ne Danilo ya jefa kwallon farko a minti na 50.

A minti na 58 Sassuolo ta farke kwallonta ta kafar Defrel inda wasan ya koma kunnen doki 1-1.

A minti na 82 Ramsey ya jefa kwallo a raga inda Juventus ta wuce gaba da kwallo 1.

A minti na 92 kuma dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ya jefa kwallo ta 3 a ranar Sassuolo.

Juventus ta samu nasarar wasanni 3 a jere inda ta ke da maki 33 a matsayi na 4 a gasar.

Sassuolo kuma na da maki 29 a matsayi na 7.

News Source:   ()