Korana ta kama Mensah dan wasan Kungiyar Besiktas

Korana ta kama Mensah dan wasan Kungiyar Besiktas

Kungiyar kwallon kafar Beşiktaş ta kasar Turkiyya ta sanar da cewa dan wasanta dan kasar Ghana Bernard Mensah ya kamu da kwayar cutar Corona.

Shugaba sashen lafiya ta kungiyar Dkt. Tekin Kerem Ülkü, ya bayyana cewa daya daga cikin yan wasan kungiyar dan kasar Ghana mai suna Bernard Mensah ya kamu da kwayar cutar Corona. 

 Sanarwar ta kara da cewa tuni an dauki matakan da suka dace domin samun lafiyar Bernard Mensah.

 

News Source:   ()