Liverpool za ta sayi dan wasan Turkiyya da ke saka riga a Schalke 04

Liverpool za ta sayi dan wasan Turkiyya da ke saka riga a Schalke 04

Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Liverpool ta bude aljihunta don sayen dan wasa dan kasar Turkiyya Ozan Kabak, wanda ke taka leda a kungiyar Schalke 04.

Mai horar da 'yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ne ya nace kan sai sun sayi dan wasan, kuma kungiyar ta ware fan stalin miliyan 20 don baiwa kungiyar ta Jamus.

Za a yi amfani da dan wasan Turkiyya wajen maye gurbin Virgil van Dijk da ba ya buga wasanni na tsawon watanni 6 saboda raunin da ya samu.

Ba don matsalar da annobar Corona ta janyowa kungiyar ba, da a kakar wasanni ta bana za a kammala cinikin dan wasan.

Kafin annobar Corona ta bulla Schalke 04 ta bayyana farashin dan wasan kan kudi fan stalin miliyan 40.

Liverpool kuma ta shirya sayen dan wasan kan fan miliyan 20.

A watan Janairun 2019 ne Galatasaray ta sayarwa da Stuttgart dan wasan kan kudi Yuro miliyan 11, a kakar wasanni ta wannan shekarar ya koma Schalke 04 kan kudi Yuro miliyan 15.

News Source:   ()