Los Angeles Lakers sun lahe gasar NBA

Kungiyar Los Angeles Lakers da ke Amurka ta lashe gasar NBA ta kakar wasanni ta bana.

A wasa na 6 na jerin wasannin da aka buga, Lakers ta fafata da Miami Heat inda ta yi farin ciki bayan shekaru 10.

A kashin farko na wasan Lakers ta fara jagorancin nasarar gasar.

Wannan ya sanya tun da fari Miami ta fara rashin nasara.

An kammala kashi na 2 na wasan Lakers na da ci 64 inda Miami tana da 36.

A zagaye na 3 kuma Lakers ta sake samun nasara sakamakon jefa kwallayen da Rajon Rondo ya yi, inda a zagayen na 4 na karshe kuma Lebron ya ciyo mata karin kwallaye.

A karshe dai an tashi wasan Lakers na da kwallaye 106 inda Miami ta ke da 93.

News Source:   ()