Mahalarta Gasar Wasannin Motsa Jiki ta Tokyo 2020 148 sun kamu da Corona

Mahalarta Gasar Wasannin Motsa Jiki ta Tokyo 2020 148 sun kamu da Corona

Mutane 148 aka samu dauke da kwayar cutar Corona a lokacin da ake ci gaba da tantance mahalarta Gasar Wasannin Motsa Jiki ta Tokyo 2020 da za a gudanar a Tokyo Babban Birnin Japan.

Kwamitin Shirya Gasar ya bayyana cewa, an samu karin mutane 15 da suka je kasar dauke da cutar ta Corona.

An bayyana cewa, mahalarta wasannin ba sa zaune a unguwar Harumi da ke gabar tekun Tokyo.

Daga ciki wadanda suka kamu da Corona a Tokyo har da jami'an gwamnatoci 8 da ma'aikatan 'yan kwantiragi 4.

An killace mutanen da suka kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu jimillar mutane 148 aka samu dauke da Covid-19. Ana ci gaba da tantance mahalarta gasar.

News Source:   ()