Mai horar da 'yan wasan Gaziantep FK ya nemi a ba shi izinin zama dan kasar Turkiyya

Mai horar da 'yan wasan Gaziantep FK ya nemi a ba shi izinin zama dan kasar Turkiyya

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Gaziantep FK, Marius Sumudica ya bayyana bukatarsa ta zama dan kasar Turkiyya.

Shugaban Kungiyar Gaziantep FK, Mehmet Buyukes ya shaida cewa, a kwanakin da suka gabata Sumudica ya nemi da a ba shi damar zama dan kasar Turkiyya.

Buyukes ya ce, sakamakon haka an yi dukkan abubuwan da suka kamata.

Ya ci gaba da cewa "Wannan batu ne da Sumudica da kansa ya nema.  Abokanmu sun kammala komai tare da tattara dukkan takardun da ake bukata don ya zama dan kasar Turkiyya. Abokanmu sun mika takardun ga mahukuntan Turkiyya. Daga yanzu mahukunta ne za su ci gaba da aiwatar da al'amarin."

 

News Source:   ()