Makkelie ne zai yi alkalancin wasan Turkiyya da Italiya

Makkelie ne zai yi alkalancin wasan Turkiyya da Italiya

Alkalin wasan dan kasar Holan Danny Makkelie ne zai busa wasan farko na Gasar Kasashen Turai karo na 16 (EURO 2020) da Turkiyya da Italiya za su fafata.

Sanarwar da aka fitar daga shafin yanar gizo na UEFA ta ce, Hessel Steegstra da Jan de Vries ne za su taimakawa Makkelie wajen yin alkalancin wasan.

Kevin Blom kuma zai zama mataimakin alkalin wasa mai kula da bidiyo.

Alkalin wasa na 4 na fafatawar kuma shi ne Stephanie Frappart dan kasar Faransa.

A ranar Juma'a 11 ga Yuni da misalin karfe 22.00 agogon Turkiyya za a buga wasan farko na Gasar Kasashen Turai ta EURO 2020 tsakanin Turkiyya da Italiya a filin wasanni na birnin Rome.

News Source:   ()