Makomar Luka Modric a Real Madrid

Makomar Luka Modric a Real Madrid

Dan wasan kwallon kafa na tsakiya mai sanya riga a kungiyar real Madrid Luka Modric ya bayyana cewar yana matukar farin cikin kasancewa a kungiyar.

Modric ya ce rayuwarsa ta kwallon kafa na zuwa karshe inda ya kara da cewa "Akwai nasarori da dama da zan samu tare da Real Madrid."

Dan kwallon kafar dan kasar Kuroshiya ya bayyana cewar yana son ci gaba da kasancewa tare da Real Madrid, amma idan akasin haka ya afku zai nemi abubuwan da za su faranta masa.

Modric ya kuma ce bai sakawa kansa wata iyaka ba, amma zai ci gaba da sanya riga ga kungiyar kwallon kafa ta kasarsa.

Yarjejeniyar dan wasan mai shekaru 35 da Real madrid za ta kare a 2021, kuma har yanzu bai sake sanya hannu kan sabuwar kwantiragi ba.

News Source:   ()