Rossi ya kamu da cutar Corona

Rossi ya kamu da cutar Corona

Kwararren dan tseren gasar motoci  ta MotoGP da ya lashe gasar sau 9 Valentino Rossi ya fitar da sanarwa inda ya gasgata labarin da aka fitar na ya kamu da cutar Corona (Covid-19).

A gwajin farko da aka yi wa dan wasan dan kasar Italiya ba a same shi dauke da cutar ba, amma bayan an yi gwaji na biyu sai aka gano yana dauke da Corona.

Rossi ba zai halarci gasar Aragon Grand Prix da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa ba.

Kamfanin Yamaha ya fitar da sanarwa game da batun.

Yamaha ya bayyana cewar Valentino Rossi bai samu damar halartar tseren France Grand Prix da aka yi ba saboda mamakon ruwan sama da aka samu.

News Source:   ()