Serena ta janye daga gasar US Open

Serena ta janye daga gasar US Open

Shahararriyar Ba'amurkiya 'yar kwallon tennis Serena Williams ta bayyana janyewa daga zagaye na 22 na gasar tennis ta kasa da kasa inda ta ce ba za ta iya halartar zagayen US Open ba saboda raunin da ta samu.

Williams ma shekaru 39 a fita daga wasan farko da suka buga tun a awa dayan farko wanda tun daga sannan ta dakatar da fita filin wasa.

Williams ta bi jerin su Roger Federer, Rafael Nadal da Dominic Thiem wadanda dukkan su ba za su samu damar kammala gasar US Open 2021 ba.

Williams da ta taba lashe gasar sau 6 ta fitar da wata sanarwa ta shafinta na Instagram cewa,

"Duba da shawarwarin da likitoci da ma'aikatan lafiyarmu suka bayar, dole na bar gasar US Open saboda ciwon da na ji  ya warke gaba daya."

 

News Source:   ()