Shahararren dan kwallon kafa na Brazil, Pele ya rasu

Duniyar kwallon kafa na makoki...

Shahararren dan kwallon kafa na Brazil, Pele ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

Gwamnatin Brazil ta aiyana kwanaki 3 na zaman makoki a kasar bayan da Pele ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

Edson Arantes do Nascimento, dan wasan kwallon kafa da aka fi sani da Pele kuma wanda ya samu gagarumar nasara a tarihin kwallon kafa, ya mutu a asibitin Albert Einstein inda aka yi masa jinya a birnin Sao Paulo.

Pele ya ci kwallaye dubu 1 da 281 a tsawon rayuwarsa.

Ya kafa tarihin da ke da wuyar dokewa.

Pele da aka haifa a ranar 23 ga watan Oktoban shekarar 1940 a Brazil, ya nuna bambancinsa a kowane lokacin da ya taba kwallo.

Pele, wanda ya kasance mai gyaran takalma har zuwa lokacin da aka gano baiwarsa ta kwallon kafa yana da shekaru 11, ya buga wasansa na farko a shekarar 1956.

Bayan shekaru biyu, da ya ke shekara 17, ya shiga Gasar Cin Kofin Duniya tare da rigar tawagar kasar.

Ya taka rawar gani a nasarar da Brazil ta samu inda ya zura kwallaye 2 a ragar Sweden da ta karbi bakuncin gasar.

Wannan nasarar ta sa ya yi suna a duniya.

Gasar Cin Kofin Duniya da aka gudanar a kasar Mekziko a shekarar 1970, wanda ya kara sa Pele shahara, ya kasance Gasar Cin Kofi Duniya ta farko da aka watsa a talabijin na zamani mai kala.

Bayan da ya lashe Gasar Cin Kofin Duniya sau 3 a tsawon rayuwarsa, Pele ya ci kwallaye 5 a wasa 1 sau 6 a tsawon rayuwarsa.

Fitaccen dan wasan kwallon kafan, wanda ya zura kwallaye 4 a wasa 1 sau 30, ya kuma zura kwallaye 3 a wasanni 92 da ya buga.

Sarkin Kwallon Kafa, Pele, ya taka leda a Kungiyar Sao Paulo Santos FC tsakanin shekarun 1956 da 1974.

A lokacin, yawancin kungiyoyin Turai sun so su sauya Pele.

Sai dai Gwamnatin Brazil ta aiyana tauraron dan wasan a matsayin "taska na kasa" kuma Pele bai iya komawa kasar waje ba.

Wani abun da ya fi jan hankali a rayuwar fitaccen dan wasan kwallon kafan shi ne yadda aka aiyana tsagaita wuta na kwanaki 2 a Yakin Basasar Najeriya domin kallon wasan Pele...

News Source:   ()