Tokyo 2020: 'Yar wasan dambe ta Turkiyya ta isa wasan quater final

Tokyo 2020: 'Yar wasan dambe ta Turkiyya ta isa wasan quater final

'Yar wasan dambe ta Turkiyya Buse Naz Cakiroglu ta isa wasan quater final a gasar dambe ta mata da ake yi a wajen wasannin motsa jiki na Tokyo 2020.

A wasan 'yan 16 Buse Naz ta kara da 'yar Uzbekistan Tursunoy Rakhimova a filin wasa na Kokugikan Arena.

'Yar damben ta Turkiyya mai shekaru 25 ta doke abokiyar karawarta 'yan Uzbekistan da ci 3 da 2.

A wasan quater fina Buse Naz za ta kece raini da 'yar kasar Taylan Jutamas Jitpong wadda ta doke 'yar kasar Filifin Irish Magno da ci 5 da nema.

A ranar 1 ga Agusta ne za a buga wasan na quater final wanda in har Buse Naz ta yi nasara za isa ga wasan semi finai.

News Source:   ()