UEFA: Za a canja dokar bayar da nasara ga wanda ya fi yawan kwallaye a gidan abokin karawarsa

UEFA: Za a canja dokar bayar da nasara ga wanda ya fi yawan kwallaye a gidan abokin karawarsa

Daga kakar wasanni ta 2021/2022 a gasar Zakarun Turai, an daina aiki da dokar bayar da nasara ga kungiyar da ta fi yawan jefa kwallaye a gidan abokiyar karawarta.

Sanarwar da aka fitar daga UEFA ta bayyana cewa, za a canja dokar nan wadda ta ke bayar da damar yin nasara ga kungiyar da ta fi yawan jefa kwallaye a wasan da suka buga a gidan abokiyar karawarta

Daga yanzu dokar za ta koma kamar ta wasa daya tilo inda idan aka yi kunnen doki a wasa na 2 za a kara lokaci mai zagaye 2 da ke da mintuna 15 kowanne. Idan kuma a karin lokacin babu wanda ya haura wani da kwallaye sai a yi bugun daga kai sai mai tsaron gida.

 

News Source:   ()