Za a kammala zagaye na 14 na gasar MotoGP a Portugal

Za a kammala zagaye na 14 na gasar MotoGP a Portugal

An bayyana cewar za a gudanar da zagaye na karshe kuma na 14 na gasar tseren babura ta kasa da kasa ta MotoGP a kasar Portugal.

Za a gudanar da gasar a filin tsere na Algarve mai tsayin kilomita 4,6, kuma za a fara jera babura da misalin karfe 17.10 na ranar Juma'ar nan agogon Turkiyya.

Za a gudanar da gasar a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba da misalin karfe 17.00, inda za a kwaya har sau 25.

A makon da ya gabata matukin Suzuki Ecstar dan kasar Spaniya, Joan Mir ne ya yi nasara.

 

News Source:   ()